Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, CON Sarkin Kano MURNAR AIKIN AL’UMMA: DIGIRIN ‘DOCTOR OF PHILOSOPHY’ Ph.D UNIVERSITY OF LONDON




A yau hudu ga watan Satumba 2025, Allah Ya ni’imata Mai Martaba Khalifah Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano da karin cigaba a rayuwarsa ta aikin al’umma Jama’ir London tayi bikin bashi digirinsa na PhD. A wannan digiri yayi rubutu akan dokar Shari’ar Musulunci da tasirinta wurin kawo kyakyawar zamantekawar al’umma ya kwantata yunkurin da ya yi a Masarautar Kano da kuma wanda Masarautar Morocco ta yi. Wannan aikin ya nuna kasancewar tsahon rayuwarsa shi mai neman ilmi tun farkon da kuma himmarsa ta yadda zaiyi amfani dashi don cigaban al’umma.
Wannan marhala ta rayuwar Mai Martaba ta nuna jajircewarsa masaman saboda kalubalan da ya fuskanta da ya shafi karagar mulki da yadda siyarsa kasa juya shi da kuma barazanar da fuskanta a rayuwarsa kuma duk ba su hana shi cigaba da neman ilmi don inganta zamantakewar al’ummarsa ba.

Wannan nasarar kamala karatu ba kawai cigaba ne a gareshi ba har ma ga al’umma baki daya saboda wannan shi ne abinda magabata suka kafa tubulin gina wannan al’umma da shi kuma suka dora mabiya nagari a kai. Tarihi ya tabbatar cewa jagoranci nagari da samun cigaban al’umma ba za a sami su ba sai da ilmi. Kuma Mai Martaba ya tafiyar da rayuwarsa gaba daya akan wannan kudurin.

Bikin karba wannan digiri ya hada da abubuwan karamawa da girmama Mai Martaba daga ciki akwai liyafa rana tare da shugaban jami’ar London (Vice Chancellor and President University of London) da sauran manyan ma’ikatan jami’ar da kuma wasu manyan mutane. Sannan kuma da daddare ‘yan uwa da abokan arziki sun shirya liyafar murna ta mutum 150 a Lanesborough Hotel London.

Yayin da yan Nigeria da sauran mutanen duniya suke taya Mai Martaba murnar wannan cigaba a marhala ta rayuwarsa mai albarka, mu ma yan uwansa muna farin ciki da murna saboda gudumarwar da yake bayarwa, da kuma jajircewasa da rashin tsoro da kuma daukakar da Allah Yayi masa. Rayuwarsa abar misali da koyi ce ga matasa da sauran al’umma kuma ta nuna cewa da ilmi da al’adu nagari suna iya haduwa don cigaban al’umma.

Muna taya Mai Martaba murna, Allah Yaja zamaninsa Sarki, Allah Ya taimaki Sarki, Allah Ya karawa Sarki imani da lafiya. Allah Ya jikan magabata. Allah Ya karawa Mai Babban Daki lafiya da imani.
Yan Uwan
Mai Martaba Khalifah Muhamad Sanusi II
Sarkin Kano.

Comments

Popular posts from this blog

Stakeholders Urged To Promote Sports As Government College Wins Femi Gbajabiamila U-16 Football Tournament

Exclusive: How Former Minister Malami and Ex-Rep Shehu Koko Imported Notorious Bandits to Destabilise Kebbi ***Meet Waterloo in the Hands of Angry Residents, APC Supporters

Dorcas Adeyinka Sues Olumuyiwa Adejobi, Nigerian Police Over Alleged Abuse Of Fundamental Human Rights